![]() |
Pep Guadiola |
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Machester City, Pep Guardiola ya ce ba ya ganin kungiyar za ta lashe gasar zakarun nahiyar Turai "Champions League" amma ya yi imanin cewa kungiyarsa tafi karfin Real Madrid da Bayern Munich in har ta hadu da su a wata mai zuwa.
Man City dai ta fafata wasa a zagaye na biyu inda ta doke Club Brugge da ci 3-1 a ranar Laraba a gasar "Champions League" don kaucewa fadawa cikin waɗanda suka fice daga gasar sakamakon rashin kokari.
Kazalika City karfinta ya ragu a gasar Premier a wannan shekarar, inda take a mataki na hudu da maki 12 tsakaninta da Liverpool da take a mataki na 1.