Kwamitin hadaka na majalisun dokokin Nijeriya ya bukaci hukumar shirya jarabawar shiga jami'a JAMB ta yi bayani akan yadda ta kashe makudan kudade wajen siyen abinci da, kayan makulashe da maganin sauro da wasu abubuwan cikin shekara ta 2024 da suka kai naira biliyan 1.85.
Kwamitin ya kuma yi barazanar katse kudaden da hukumar za ta karba daga gwamnatin tarayya a cikin 2025.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana a gaban majalisar domin gabatar da kasafin kudin 2025.
Category
Labarai