Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ayyana kujerar dan majalisa mai wakiltar Talatar Mafara ta Kudu Aliyu Kagara, a matsayin babu kowa a kanta saboda rashin halartar zaman majalisa a lokaci daban-daban.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na majalisar Bello Kurya ya fitar, ta ce an dauki matakin ne saboda cikin zama 180 da majalisar tayi, sau 21 kawai dan majalisar ya halarci majalisar.
Sanarwar ta ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki na Nijeriya kuma majalisar ta nada kwamitocin domin zama da dan majalisar amma abin ya ci tura.
Category
Labarai