Shugaban majalisar Dokokin jihar Bauchi |
A wani ci gaban fasaha, majalisar dokokin jihar Bauchi ta kafa tarihi inda ta tantance mutum na farko da gwamnan jihar ya tura da sunan sa a matsayin kwamishina Usman Usman Shehu, ta na'urar Internet na Video wato Zoom.
Wannan ya nuna kudurin majalisar dokokin jihar na rungumar sabon tsari a cikin al'amuran ta, da tabbatar da rungumar fasahar zamani cikin ayyukanta.
Usman Usman Shehu, wanda dan karamar hukumar Giade ne ta jihar Bauchi, ya fara karatunsa na farko da karatun Islamiyya kafin ya wuce makarantar firamare da sakandare a jihar. Ya ci gaba da neman ilimi har zuwa jami'a a yanzu yana zaune a kasar Jamus.
Duk da anyi tantancewar ta hanyar Zoom a majalisar amma ba a samu wata matsala, inda membobin majalisar suka yi tambayoyi masu muhimmanci tare da samun ingantacciyar amsa daga Usman Usman Shehu.