Akalla mutane uku ne rahotanni ke nuna cewa sun riga mu gidan gaskiya bayan da wasu mahara suka kai farmaki tare da awon gaba da mutum 24 a wasu kauyuka hudu na karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Dailytrust cewa yaran Bello Turji ne suka kai harin a garin Shinkafi, Jangeru, Shanawa da Birnin Yero a ranar Alhamis.