Mahara sun yi ajalin mai tsaron lafiyar shugaban karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina


Wasu mahara da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi ajalin wani jami'in tsaro a harin da suka kai gidan shugaban karamar hukumar Malumfashi Shamsudden Lawal, a jihar Katsina.

Maharan sun tafka wannan ta'asar ne cikin daren ranar Talata kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Sai dai babu rahoton ko harin ya shafi wasu amma dai an fatattaki maharan ba tare da sun samu nasarar tafiya da kowa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp