![]() |
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce hukumar karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Sale Usman tare da manyan sakatarorinta da masu ruwa da tsaki sun cimma matsaya bisa duba na tsanaki kan kudin da kowane Alhajin Nijeriya zai biya a shekarar 2025.
A cewar sanarwar mahajjatan da suka fito daga shiyyar Borno da Adamawa,za su biya Naira miliyan 8.3.Hakazalika, maniyyatan da suka fito daga jihohin Kudu za su biya Naira miliyan 8.7.
Sai kuma alhazan da suka fito daga yankin Arewa za su biya Naira miliyan 8.4.
Shugaban hukumar Farfesa Saleh ya bukaci mahajjatan da suke son zuwa aikin Hajji da su bi dukkan ka’idojin kasar Saudiyya ta gindaya tare da jaddada muhimmancin biyan kudi da wuri da kuma yin rajista a kan lokaci.