Babban bankin Nijeriya ya yi karin haske cewa, ma'aikata 1000 da su ka bar aiki a shekarar 2024 ba tursasa su aka yi ba don su ajiye aiki.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso, ya sanar da hakan a gaban kwamitin bincike na majalisar wakilai da ke bincike akan dalilin barin aikin ma'aikatan da kuma yadda aka amince da biyansu naira biliyan 50 a matsayin hakkinsu na barin aiki.
Cardoso ya ce duk wadanda abin ya shafa sun ajiye aiki ne bisa radin kansu, karkashin wani shiri na biyan ma'aikata duk hakkokinsu idan su ka ajiye aiki da wuri.