Likitocin da ke yajin aiki a Abuja sun ƙalubalanci Minista Wike da Sanata Akpabio su je asibitin gwamnati a duba su


Kungiyar lokitoci dake yajin aiki a babban birnin tarayya Nijeriya sun ƙalubalanci Ministan Abuja Nyesom Wike da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da su je asibitocin gwamnati domin a duba su kuma su gane wa kansu irin wahalar da jami'an kiwon lafiya da marasa lafiya ke sha.

Da yake zanta wa da gidan talabijin na Channels, shugaban kungiyar likitocin George Ebong, yace idan har manyan ƙasar nan ba su amfani da asibitocin gwamnati to ba za ayi gyara a fannin kiwon lafiya ba.

A wannan Laraba ne dai likitocin suka soma yajin aikin gargadi na kwana uku saboda kin biyan albashi da alawus alawus dinsu da dai sauran bukatu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp