![]() |
Likitoci |
Likitocin birnin taraiya Abuja sun tsunduma yajin aiki a ranar Larabar nan sakamakon rashin biyansu albashin watanni 7 na aikin da suka yi a shekarar 2023.
Wakilin Daily Trust da ya ziyarci babban asibitin Kubwa da ke Abuja ya shaida yadda wasu majinyata ke fãma saboda rashin damar ganin likita.
Sai dai wasu masu lura da asibitin sun ce yajin aikin da ake yi zai dauki tsawon kwanaki uku ne a matsayin na gargadi, kuma akwai yuwuwar aci gaba dayi idan gwamnati ta gaza biyan bukatun likitocin.
Ko a kwanakin baya kungiyar likitocin ta yi gargadi ga ministan babban birnin tarayyar Najeriyar Nyeson Wike bisa shiga yajin aikin kwanaki 14 a ranar 23 ga watan Disambar 2024, inda suka bukaci ya gaggauta daukar mataki tare da biyan bukatun na su.