Malam Nuhu Ribadu |
An bukaci mai baiwa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya yi amfani da kwarewa wajen kawo karshen ‘yan bindiga, Bello Turji, a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.
Kungiyar matasan Arewa da samar da zaman lafiya da ci gaban siyasa hadin gwiwa da kungiyar dattawan Arewa ne suka yi kiran a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen taron hadin gwiwa karo na 8 da suka gudanar a Kaduna ranar Alhamis.
Sanarwar wadda Yusuf Abubakar, da Alhaji Yasir Ramadan Kano, kungiyar matasa da kungiyar dattawan Arewa suka sanya wa hannu, ta kara da yin kira ga shugabannin siyasa da masu fada aji da su hada kai domin samar da mafita mai dorewa ga al’umma da kalubalen da yankin ke fuskanta.
Sai dai sun yi kira ga malaman addini da su daina amfani da kalaman da za su tunzura al'ummar ko kuma su haifar da gaba a tsakanin su ba tare da la'akari da abubuwan da ke faruwa ba.
A cikin sanarwar sun yaba wa mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu,bisa namijin kokarin da yake yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin kasar, musamman a yankin Arewa.
A karshe sun yi kira ga Malam Ribadu da ya yi amfani da kwarewr aiki wajen kawo karshen ‘yan bindiga da Bello Turji a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.