Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa ta Nijeriya na son a rage ƙarin kudin kira da na data zuwa kashi 10 ko su tafi kotu

Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa ta Nijeriya NATCOMS ta ce za ta dauki matakin shari'a kan hukumar sadarwar Nijeriya NCC, biyo bayan kin amincewar bukatar rage karin kudin kira da data daga kaso 50 zuwa kaso 10.

Yayin zantawarsa da jaridar Punch a ranar Talata, shugaban kungiyar Adeolu Ogunbanjo ya ce halin ko in kula na NCC ya jefa masu amfani da layukan sadarwa cikin zulumi na karin kudaden.

"Mun basu zuwa jiya Talata cewa su fada mana matsayarsu amma har yanzu shiru, ba don haka zamu garzaya zuwa kotu a yau Laraba" in ji Adeolu.

Kungiyar ta NATCOMS na wakiltar al'ummar Nijeriya Miliyan 157 dake amfani da layukan sadarwa daban-daban.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp