Kungiyar kwadago NLC a Nijeriya ta dage akan cewa dole sai gwamnatin tarayya ta janye dokar garambawul ga haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar.
A cikin sakonta na barka da sabuwar shekara, Shugaban kungiyar NLC Joe Ajaero ya ce wannan ya zama dole saboda inganta walwalar ma'aikatan Nijeriya.
Ya kuma jaddada muhimmancin aikin gwamnati a buɗe tare da janyo masu ruwa da tsaki da kuma yi wa 'yan kasa adalci a kowane lamari.