Kungiyar kwadago ta NLC na shirin gudanar da zanga-zanga ta kasa a ranar 4 ga watan Fabrairu kan karin kudin kira da data dana tura sakonni da gwamnatin tarayya ta yi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar ta amince da yin zanga-zangar ne a yayin taron shugabannin NLC na kasa dake gudana.
Matakin wani jan kunne ne ga gwamnati cewa ma'aikata za su ci gaba da kalubalantar karin kudin saboda yanayin talauci da zai kara jefa al'ummar kasar.
Category
Labarai