![]() |
FIRS Chiarman |
Shugaban hukumar tattara haraji ta Nijeriya FIRS, Zacch Adedeji, ya bayyana cewa, hukumar ta tara naira tiriliyan 21.6 na kudaden haraji, wanda ya zarce N19.4 da tayi hasashen samu a shekarar 2024.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis a yayin taron da ya gudana a Abuja.
Taron an tsara shi don tattauna mahimman abubuwan da za ta mayar wa hankali don cimma burin hukumar na 2025.
A cewarsa, a shekarar 2024, hukumar ta FIRS ta tsara shirin samun kudaden haraji na N19.4tn amma ya zarce kashi 11.34 bisa 100, inda aka tara naira tiriliyan 21.6.