Kudaden FAAC da gwamnatocin Nijeriya ke rabawa sun ragu da biliyan N303 a watan Disamban 2024


Gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomin Nijeriya sun raba kudaden shiga da kasar ta samu a watan Disamban 2024 da yawansu ya kai naira tiriliyan 1.424. 

Sai dai idan aka kwatanta da naira tiriliyan N1.727 da aka raba na watan Nuwamba, an samu ragin naira biliyan N303, kusan kashi 17.54 kenan, a cewar jaridar Punch.

Wani bayani da daraktan yada labarai na ofishin Akanta Janar na tarayya Bawa Mokwa ya fitar, ya ce an raba kudaden ne a yayin zaman kwamitin rabon tattalin arzikin kasa FAAC da aka gudanar a Abuja a wannan Jumu'ar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp