Kotu ta haramta wa hukumar kiyaye hadurra a Nijeriya cin tarar direbobi ko kama abin hawa da lambarsa ta dusashe


Wata babbar kotu dake zamanta a Lagos ta hana wa hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC cin tarar direbobi ko kama abin hawa da lambarsa ta dusashe.

Mai shari'a Akintayo Aluko ya bayar da wannan umurnin a wannan jiya jumu'a, yayin da yake yanke wannan hukunci ne kan karar da wani lauya Chinwike Chamberlain Ezebube ya shigar akan hukumar ta kiyaye hadurra FRSC.

Kotun ta ce hukumar ba ta da hurumin cin direbobin da lambar abin hawansu ta disashe har sai ta karbi umurni daga wata kotu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp