An tisa keyar wata mata mai suna Dumsile Dludlu gidan yari har na tsawon shekaru uku saboda laifin leken asirin sakwannin mijinta na manhajar WhatsApp ba tare da izininsa ba.
Laifin da matar ta aikata ya saba ma dokar laifuka ta yanar gizo a kasar Eswatini.
Hukuncin wanda mai shari’a Fikile Nhlabatsi ya yanke a kotun majistare dake babban birnin kasar Mbabane.
Za a ci gaba da shari'ar a ranar 10 ga Maris, 2025.
Category
Labarai