Babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta amince da bukatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na yin kwaskwarima kan tuhumar da ake yi wa tsohon ministan wutar lantarki, Dakta Olu Agunloye.
Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya amince da gyaran ne yayin da yake yanke hukunci kan rashin amincewar wanda ake kara kan karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Yuni, 2024.
Dakta Olu Agunloye dai na fuskantar tuhumar laifuka bakwai da EFCC ta shigar a gaban kotu mai lamba FCT/HC/CR/617/2023.
Laifukan sun shafi na jabu, kin bin umarnin shugaban kasa, da kuma aikata almundahana da suka shafi aikin tashar wutar lantarki ta Mambila a jihar Taraba.