Nijeriya ta yi nasara a shari'ar da kasar ke yi kan kudaden makamai sama da dala miliyan 6 da kasar Amurka ta karbe a shekara ta 2014, a zamanin mulkin tsohon Shugaba Jonathan.
Amurka ta kwace kudaden ne saboda tayi Zargin a na kokarin sayen makamai a hannun wani kamfani maras lasisi, abinda ya sabawa dokar kasar.
A hukuncin da ta yanke a ranar 23 ga watan Disamban 2024, Kotun dake gabashin jihar California, ta amince a mayar wa Nijeriya kudaden da yawansu ya kai dala miliyan $6.02.