Rahotanni na nuni da cewa ƙasurgumin ɗan bindiga ‘Baƙo-Baƙo’ ya baƙunci lahira a wannan Alhamis, yayin wani farmaki da jami'an tsaro na hadin gwiwa su ka kai a dajin Batsari dake jihar Katsina
Majiyoyin tsaro sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa an tafka ƙazamin faɗa kafin jami'an soji da 'yan sanda da civil defence da jami'an tsaron al'umma na Katsina su samu nasarar cin ƙarfin yaran ‘Baƙo-Baƙo’ kuma aka kashe shi.
Category
Labarai