![]() |
Daliban Firamare |
Shugaban ofishin UNICEF mai kula da shiyyar Kano, Rahama Mohammed, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025 a ranar Juma’a a Kano.
A cewarsa, jihar na fama da matsananciyar matsalar ilimi, inda yara kusan miliyan daya ba sa zuwa makaranta, bisa ga sabbin bayanai da suka fito.
Ya ce a halin yanzu kusan kashi 32 cikin 100 na yara ne ba sa iya shiga makarantun sakandire zuwa gaba da sakandire a jihar,don haka akwai bukatar ayi adinda ya dace wajen rage kason wa'yanda ba sa iya tsallake wannan mataki.