A ci gaba da ziyarar da yake yi a wasu kasashen, Shugaba John Dramani Mahamma ya sauka kasar Sénégal inda ya gana da takwaransa na Sénégal Bassirou Diomaye Faye.
A yayin ziyarar wadda ke zuwa 'yan kwanaki bayan Mahamma ya sha rantsuwar kamun aiki, shugabannin biyu sun tattauna batun karfafa danganta su a fannoni daban daban ciki har da karfafa tsaro a yankin Sahel da ma ECOWAS.
Category
Ketare