Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi/Shugaba Tinubu |
Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan tattaunawa da Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a fadar sa dake Abuja.
Ya ce ta hanyar hadin kai da taimakon juna ga kasashen duniya ne za a iya kawo karshen kalubalen tsaro.
A cewar sa kasar China na son yin aiki tare da kasashen Afirka wajen aiwatar da shirin samar da tsaro da zaman lafiya a duniya,inda ya ce kasar tasu a shirye take ta bayar da gudun mawa wajen inganta tsaro a nahiyar Afirika.