Matatar mai ta Dangote ta danganta karin kudin man fetur da ta yi da hauhawar farashin danyen mai ke yi kasuwar duniya.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsu na Facebook, ta ce domin saukaka wa 'yan Nijeriya karin 50% matatar kawai ta yi daga cikin karin da mai ya yi a kasuwar duniya.
Matatar ta jaddada kudurinta na samar da man fetur cikin sauki ga al'ummar Nijeriya.
Category
Labarai