Kano Pillars ta doke abokiyar hamayya ta Enyimba da ci 2-0, a wasan cike gurbi na mako na 14 na gasar firimiyar Najeriya NPFL ta kakar wasannin 2024/25.
Dan wasa Abba Adam ne ya zura kwallaye biyun a mintuna na 26 da 72, da hakan ya bawa kungiyar ta sai masu gida gagarumar nasara akan abokiyar burminta.
Shin kuna ganin Pillars zata iya lashe gasar firimiyar NPFL a bana?