Jam'iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ta yi kira ga shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu da ya yi bincike tare da ƙwato sama da Naira tiriliyan 25 da ake zargi mukarraban gwamnatin APC sun sace.
Wannan na kunshe ne a cikin sakon barka da sabuwar shekara da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar PDP, Debo Ologuagba ya fitar.
Jam'iyyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya magance matsalolin tsaro da hauhawar farashin kayan abinci domin rage wahalhalun da 'yan Nijeriya ke fuskanta.