Wani farmaki da jiragen rundunar sojin saman Nijeriya suka kai a maboyar 'yan ta'adda ya yi sanadiyar mutuwar wadanda ake zargin 'yan bindiga da dama a dajin Alawa Forest cikin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Rundunar ta ce an kai harin ne karkashin rundunar Operation Fansan Yamma dake yaki da 'yan bindiga a yankin Arewa ta Yamma da Arewa ta Tsakiyar Nijeriya.
Sanarwar da daraktan yada labarai na ofishin rundunar sojin saman Olusola Akinboyewa, tace an tarwatsa maboyar 'yan bindigar.
Category
Labarai