Kwamishinan albarkatun kasa na jihar Bauchi Alhaji Mohammed A Bello da takwaransa na jihar Gombe Alhaji Sanusi Ahmed Pindiga sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara ɗibar ɗanyen mai a rijiyar Kolmani da aka kaddamar shekaru biyu da suka gabata.
Kwamishinonin biyu sun bayyana hakan ne a wata hira da manema da manema labarai a ofisoshinsu a kebance.
Sun bayyana cewa gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe na iya kokarinsu ganin cewa kamfanin da aka baiwa kwangila ya dawo ya ci gaba da aiki.