Gwamnatin jihar Kano, ta soki tare da yin watsi da kudirin garambawul ga dokar haraji da ke gaban majalisar dokoki a yanzu haka.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan ta bakin mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo, da hakan ya bayyana matsayar gwamnatin a yayin bikin sabuwar shekara ta 2025.
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, ta ce jihar Kano ba ta goyon bayan dokar saboda za ta shafi walwalar al'umma, tare da kara jefa su cikin halin kaka nikayi.