Jam'iyyar APC mai mulkin jihar Kaduna ta bukaci jam'iyyar PDP ta guje wa bata sunan APC ta hanyar yin zarge-zargen da basu da tabbas domin yada farfaganda.
APCn wadda ke martani kan zargin yunkurin hallaka Sanata Lawal Adamu Usman mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta bayyana zargin a matsayin kage.
A cikin wani bayani da Sakataren APC Alhaji Yahaya Baba Pate ya fitar, ya shawarci PDP ta rika yin adawa mai ma'ana.
Category
Labarai