Jami'in tsaron al'umma a Sokoto ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure


Wani jami'in rundunar tsaron al'umma ta jihar Sokoto da ba a bayyana sunansa ba, ya kashe kansa bayan ya yi harbi bisa kuskure bayan da jami'an tsaron hadin gwiwa su ka ceto mutum 66 da aka yi garkuwa da su.

Farmakin da sojoji su ka jagoranta ya faru ne a dajin Tidibali da ke gabashin Sokoto.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ya ce jami'in ya rasa ransa ne bayan yin harbi bisa kuskure.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp