Shugaban jami'ar Abuja Farfesa Aisha Maikudi, ta ce jami'ar na gab da soma karantar da kwas na koyon harshen Chinese da kuma al'adunsu.
Farfesa Maikudi ta bayyana hakan ne a jiya Jumu'a, lokacin da ta karbi bakuncin dalibban nazarin aikin jarida na Jami'ar Tsinghua ta kasar China da suka kai mata ziyara..
Ta ce jami'ar Abuja na da tsohuwar alaka da kasar China, kuma akwai daliban jami'ar da yanzu haka ke koyon kwasa kwasai na Mandarin.
Category
Labarai