Jami'an tsaro sun killace tare da karbe iko da sakatariyar jam'iyyar PDP a birnin Tarayya Abuja, bayan rikicin da aka yi.
Jami'an tsaron sojoji da 'yan sanda sai na civil defence ne suka karbe Iko da sakatariyar bayan hatsaniyar da ta faru ttsakanin tsagin magoya bayan Samuel Anyanwu da Sunday Ude -Okoyes kan waye halastaccen sakataren jam'iyyar ta kasa.
An fara hatsaniyar jim kadan bayan isowar Anyanwu da Ude -Okoyes a wurin taron kwamitin amintattu na jam'iyyar ta PDP.
Category
Labarai