Jami'an tsaro a kasar Korea ta Kudu , sun kama tsigaggen shugaban kasar Yoon Suk Yeol bayan da suka kutsa inda ya samu mafaka tare da kama shi.
Kamawar ta shi ta sa ya zama shugaban kasar na farko da ke kan mulki da Jami'an tsaro masu bincike na musamman suka kama.
Shugaba Yoon, mai shekaru 64 ana binciken sa ne akan saka dokar ta baci mai cike da sarkakiya a ranar 3 ga watan Disambar da ta gabata 2024, abinda ya jefa kasar cikin mummunan rikici na bore.
Kamun na shugaba Yoon, ya kawo karshen wasan buya tsakanin shugaban da Jami'an tsaron sa da na masu bincike na musamman.
Sai dai duk da tsige shugaban da Majalisar kasar tayi shugaban na cigaba da rike iko har sai Kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da tsige shi.