Iyalan wadanda harin jirgin saman Sojin Najeriya ya yi ajalin su bisa kuskure a kananan hukumomi Zurmi da Maradun a jihar Zamfara sun nemi gwamnati ta biya su diyya.
Harin wanda jirgin ya kai na ranar 11 ga Janairu 2024 a kauyen Gidan Kara da Malikawa sai Sakida tare da Kakidawa da Tungar Labbo dake Gidan Goga a kananan hukumomin na Zurmi da Maradun, ya yi sanadiyyar rayukan mutum 15 da raunata 9.
Kawo yanzu wadan da suka samu rauni na cigaba da karbar kulawar likitoci a Asibitin Kaura -Namoda dake jihar.
Daya daga cikin iyalan wanda suka nemi biyan diyyar Muhammad Aminu, a zantawar sa Jaridar Daily Trust ta wayar Tarho , ya ce suna kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta Najeriya da su gaggauta biyan su diyya sakamakon halin da aka jefa su.