Ina rokon Shugaba Tinubu ya sa baki 'yan'uwana su bani gadona - Zainab Ado Bayero

Sunana Zainab Jummai Ado Bayero, diyar mariyagi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Ina daya daga cikin 'ya'yansa kanana.


Tambaya: Ko akwai wani cigaba da aka samu bayan ganawarki ta karshe da 'yan jarida?

Babu gaskiya har yanzu. Ban samu wani taimako ba daga masarautar Kano kuma babu wani jami'i daga masarautar ta Kano da ya tuntube ni, daga bangaren dangina ko kuma bangaren Sarkin yanzu Muhammad Sanusi. Kuma ban samu wani taimako ko tallafi daga gwamnatin jihar Kano ko gwamnatin tarayya ba. Kai babu ma wanda ya taimake ni har yanzu daga Arewacin Nijeriya da ma sauran sassan kasar. Har yanzu dai muna nan inda muke cikin rikici.

Tambaya:Wane irin rikici, ko za ki iya yi mana karin haske?



A ranar 30 ga watan Disambar 2024, na dora wani bidiyo a shafina na Instagram, inda nake neman taimakon gaggawa, inda na yi bayanin cewa ba ni da inda zan zauna a Lagos, na rasa matsuguni, ban san ina zan sa kaina ba, ba mu da gida, rayukanmu na fuskantar barazana, gabadaya abin duniya ya sha min kai, na rasa inda zan sa kaina, na rasa yadda zan yi. Shi ne na yi kururuwar neman dauki. Amma kwanaki kadan bayan fitar wannan bidiyo a farkon shekarar nan ta 2025 na kara yin wata hira da gidan rediyon RFI, inda na tattauna kan matsalolin da ke damuna, cewa har yanzu ba mu da matsuguni, ba mu ma da abin da za mu ci a nan Lagos, kuma ban samu komai ba daga dukiyar mahaifina ko wani taimako daga masarautar Kano ko gwamnatin jihar Kano ko gwamnatin tarayyar Nijeriya don ceto rayuwarmu. Saboda yanzu haka muna cikin hatsari.

Tambaya: Mene ne hakikanin abin da kike bukata daga masarautar Kano?

Ina bukatar su yi abin da yake na daidai. Shekaru 10 da suka wuce bayan rasuwar mahaifina, sun hana mu gadonmu, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar jefa mu halin da muke ciki. Shekaru 10 kenan, sun rike mana gado, muna ta fadi-tashin yadda za mu yi rayuwa, mu dogara da kanmu, amma babu halin yin hakan, tun da ba mu da gida, babu damar yin karatu, babu halin yin kasuwanci bare aikin gwamnati ko na kamfani, ta yaya rayuwa za ta yiwu? A don haka, ina rokon masarautar, a matsayinmu na halastattun 'ya'ya a masarautar Kano, ina rokon a ba mu kason gadonmu ko kuma ita masarautar Kano ta samar mana da abin da za mu rika biyan bukatunmu na yau da kullum da suka hada da gida, ilmi da kuma wani abu da za mu iya dogara da shi don bukatun yau da kullum.

Tambaya: Za mu zo kan batun gado daga baya, amma idan kina maganar masarautar Kano, wasu na musun cewa me ya sa kike tunanin, ala-tilas sai masarautar Kano ta taimake ki?

Saboda ni ma Gimbiya a cikin masarautar Kano ce. Mahaifina ya yi sarki tsawon shekaru 51, kwarai kuwa, Sarki ne tsawon shekaru 51 kuma ni diyarsa ce. To ka ga kuwa ina cikin iyalan Gidan Dabo, ko suna so, ko ba su so, idan sun ce ban cancanci taimako daga gwamnatin tarayya ko ta jihar ba, ai na cancanci 'yan'uwana su taimake ni, tun da kowa ya san suna da kumbar susa, suna da kudi, masarautar Kano na da kudi. Idan na ce a taimake ni, shi ne na yi laifi, idan na roki taimako daga masarautar da ina daya daga cikin iyalinta, laifi ne?

Tambaya: Wace irin hobbasa kika yi don tunkarar 'yan'uwanki kafin ki kawo batun a kafafen yada labarai?

Shekaru da dama, suna ta alkawurra kawai, amma sun ki su cika, akwai ma mutane da dama suka da suka roke su, da su yi mana adalci, cikinsu kuwa akwai marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris, Marigayi Maitama Sule Danmasanin Kano, Marigayi Tony Momoh, wanda dan'uwa ne ga mahaifiyata. Kai akwai mutane da dama da suka roke su arziki su saurare mu, su yi mana adalci, amma duka sun yi shakulatin-bangaro.

Tambaya: Ke a kashin kanki, kin taba kokarin samunsu ku yi magana baki da baki da 'yan'uwan naki ko shi Sarkin da kansa?

Na fada maka fa, ban kai ga zuwa kafafen yada labarai ba, sai da na ga tura-ta-kai-bango, shekaru 10 da ke nan, ba su da niyyar yin abin da ya kamata, Shi ya sa nake rokon duk wanda zai iya taimaka mana da ya kawo mana dauki, ya cece mu. Saboda sun furta karara cewa su babu ruwansu ko mu mutu ko mu rayu. Ko wannan hirarrakin nawa da ke yawo, babu wanda ya ce uffan akansa daga cikinsu, me hakan ke nufi, kawai suna so ne, mu mutu a titi. Ko Sarki Sanusi, a shekarar da ta gabata mun same shi a Lagos kafin a mayar da shi Sarkin Kano, mun sanar da shi duk halin da muke ciki, ko a lokacin ya ce mana shi babu abin da zai iya yi akan matsalarmu. Ko bayan an mayar da shi Sarki ba mu hadu ido da ido ba, amma ina aike masa sako ta kafafen sadarwa, musamman a zantawata da manema labarai da aka buga a jaridu, kuma na san yana karantawa, muna tura masa sakon neman taimako, amma har yanzu shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

Tambaya: To amma, misali, ke a kashin kanki, kin taba tuntubar Sarkin Kano na 15?

Na yi wannan sau shurin masaki, kawai ba wannan ne a gabansa ba, da a ce akwai burbushin taimako a tattare da shi, da ba ma zan fito ina wannan ba. Ko wadannan faya-fayan bidiyo da ke yawo nawa, ya gansu, kuma ya san duk halin da muke ciki, babu abin da ya sha masa kai ko na mutu ko na rayu.

Tambaya: Me ya sa kike tunanin sun yi watsi da rayuwarki kamar yadda kike zargin hakan?

Wannan kuwa ai su ne za su amsa wannan tambaya. Su ne kadai suka san dalilin da ya sa suka dora mana karan-tsana. Ni dai ban sani ba, to ma, ni me na yi ma wani? 'yar karamar yarinya ce ni, me zan iya yi musu, me zan iya yi ma mutanen da ke da fada a ji, suke da karfin iko a siyasance, kai suke da duk karfin da ake da shi. To ta yaya 'yar mitsitsiya haka da ni, in ja da su. Ni dai na san ban yi wa kowa laifi ba, ban cutar da kowa ba, kawai dai ina rayuwata daidai ruwa daidai kurji, To ka ga babu dalilin da wani zai tsane ni. Ni na san ta gari ce, ban san dalilinsu na tsana ta ba, wataqila dai kawai suna bakin cikin cewa an haifo ni, wataqila don ina kokarin tsayawa da kafafuna. Ni macece, ba zan zama sarki ba, ban san dalilinsu na dora min karan-tsana ba. Kuma fa sun sha fadin cewa sun tsane ni sosai, duk kuwa da rokon da nake musu na su ceci rayuwata daga wannan rayuwa. Amma sun toshe kunnuwansu, kuma fa har kashedi suke yi wa sauran mutane cewa kada ma su tsoma baki a sha'anina. Ka da wanda ya taimake mu, a kyale mu mu mutu a titi.

Tambaya: Ko kina da sha'awar ki koma Kano da zama, misali idan aka baki zabin hakan ki, koma can ki cigaba da zama da 'yan'uwanki?

Ba zan iya komawa Kano da zama ba, saboda ba ni da tabbacin tsaron rayuwata. Mutanen nan, za su yi farinciki idan suka ga bayana. Zahirin gaskiya ba zan iya zama da su ba. Wadannan mutanen fa, labari ya tarar da su cewa a titi nake ragaita a Lagos, amma ko a jikinsu. Don me za ka ce in koma Kano in zauna da su, alhalin ba su ma son gani na a duniyar kwata-kwata? Saboda ni tsoron zuwa Kano ma nake ji, saboda wadannan mutanen. Suna iya turo wani ya kawo min hari.

Tambaya: Idan muka dubi wadannan zarge-zarge da kike cewa za ki iya rasa rayuwarki idan kika koma Kano. Wani zai yi tambaya cewa me ya sa kika nace kina bukatar taimakonsu, bayan kina tunanin za su iya cutar da ke?

Ni ba taimakonsu nake nema ba, kawai ina neman hakkina ne da nake da shi, daga mahaifina. Ina daya daga cikin 'ya'yan masarautar Kano ko suna so, ko ba sa so. Idan ba su iya fitar mana da hakkinmu ba, gwamnatin Kano na iya taimaka mana, ko kuma wannan Sarkin na yanzu ya taimaka mana daga bangaren masarauta, idan 'yan'uwana sun ki taimakawa. Hakan ba daidai bane. A kwanan nan akwai wani abu da ya faru, wani mawaki ya fito yana neman taimakon cewa rayuwarsa na cikin hatsari, kowa ya yi kunnen-uwar-shegu, sai da ya rasa ransa, sannan aka zo ana cewa a yi bincike. To yanzu gani nima ina neman taimako kowa ya yi shiru da bakinsa. Ba haka ya kamata ba.

Tambaya: Amma Zainab kin kai wannan kukan naki kotu? Saboda kin san hakkinki, me ya sa kika zabi zuwa kafafen yada labarai?


Kai ma fa dan Nijeriya ne, ina tunanin ka fahimci yadda tsarin sashen shari'a yake. Su din dai ne, baka ganin suna sauya wa tsarin shariar salo. To ni wane irin karfi gare ni da zan iya kai su gaban kuliya. Sashen shari'ar a tafin hannunsu yake, jami'an tsaron ma maganarsu kawai suke ji. Akwai wani koke da muka yi, daya daga cikinsu ya turo jami'an tsaro, aka gayyace mu, muka je caji ofis, ko yansandan ba su son su binciki lamarin nasu, ba ma sa so a sanya su cikin batun, suna cewa ba sa son yi wa masarauta laifi. To wane alkali zai iya yi min adalci? Wannan ne dalilin da ya sa suke bugun kirjin cewa sai sun ga bayana.

Tambaya: Amma kina da tabbacin wadannan zarge-zarge ba kin yi su ne don ki ci zubar musu da mutunci ba? 

Ni wa zan yi wa kage, cin zarafi ko cin mutunci? Idan na yi haka ribar me zan samu?

Tambaya: A shekarar bara, gwamnatin jihar Kano ta tallafa miki da kudin da wataqila sun kai Naira milyan 10, ko za ki iya fada mana yadda kika kashe wadannan kudade?

Tuni na yi magana kan wannan batu, bana ma son kara tattauna shi. Na yi magana ba daya ba, ba biyu ba.

Tambaya: Wannan wani abu ne musamman a Arewacin Nijeriya da ake tattaunawa a kansa cewa kin karbi tallafin Naira milyan 10 daga gwamnatin jihar Kano amma har yanzu kina neman taimako. Shi ne mutane ke diga alamar tambaya sosai!

Na fadi fa tun farko, na yi hirarraki kan wannan batu a baya, idan kana so, ka bibiyi hirarrakin da na yi a baya, kawai dai bana son na cigaba da cin tuwo da miyar bara. Na fada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiko mana da tallafin Naira milyan 10. Ni abin da nake so shi ne maslaha ta dindindin. Ni ban ma taba ganinsa ido da ido ba. Kawai dai ya aiko mai magana da yawunsa.

Tambaya: Daya daga cikin tambayoyin da mutane ke yi, ita ce me ya sa baki yi amfani da wadannan kudi da gwamnatin Kano ta tallafa miki da su ba, ki juya su ki yi kasuwanci?

Wadannan kudi, kamar yadda na ce, mun yi amfani da su ne mun biya bashi, kuma ba su isa mu sayi gida ba har ma mu yi kasuwanci.

Tambaya: Babu ko tantama, marigayi Sarkin Kano mutum ne attajiri, ko za ki iya fada mana yadda kika kashe gadon da aka raba muku?

Wannan ai shu ne abin da nake fada maka, ban samu komai daga cikin gadon da ya bar mana ba.

Tambaya: Amma kin ce kina tsoron zuwa kotu, saboda kina zargin kotu wataqila ba za ta yi miki adalci ba.

Eh kwarai kuwa, na san ma ba za a yi min adalci ba, saboda suna da karfin iko da na fada a ji. Shi ya sa ma suke jin suna iya yin duk abin da suka ga dama. Su ne ke tafiyar da ragamar kowane bangare.

Tambaya: Me ya sa kike zargin cewa sun hana ki gadonki?

To! Kamar dai yadda na ce tun farko, mutanen nan sun tsane mu. Iya abin da na sani kenan, sun tsane mu, kuma ba su son mu rayu. Abin da suke son ji ko gani shi ne, ga daya daga cikin gimbiyoyin masarautar Kano ta wulakanta. Na ma yi wani shirin talabijin na musamman kan rayuwar mahaifina, babu wanda ya kawo wani dauki wajen hada wannan shiri. An yi min zagon-kasa. Duk wani kokari da na yi na in rayu in tsaya da kafafuna, an yi tadiyeni. Ina tunanin ilhamar da Allah Ya yi min, ta in tsaya da kafafuna, na kuma fadi ra’ayina, shi ne ba su so.

Tambaya: Wane ne kike zargin shi ne ya yi uwa makarbiya wajen hana ki gadonki?

To, 'ya'yan mahaifina mana. Su ne ke rike da duk dukiya da kadarorin da mahaifinmu ya mallaka a lokacin da ya rasu.

Tambaya: Bayan wannan ganawa, mene ne fatarki?

Ina cike da fatar duk wanda Allah Ya sa ya ji kukana ya ji tausayina, ya zo ya taimake ni. Ban san zuwa yaushe za mu ci gaba da jure irin wannan rayuwar ba, saboda muna cikin hatsari, ni wallahi na ma na gaji, abin ya ci tura. Ko kuwa dai sai mun mutu sannan su taimake mu. Ina rokon gwamnatin tarayyar Nijeriya, idan ma gwamnatin jiha ba ta son taimakawa, muna rokon shugaban kasa, da Sarki Sanusi Lamido, wanda yake yawan magana kan hakkin mata, wannan matsala ce da ke ruruwa a gidansa, ya kawo mana dauki, tun da nima ‘ya ce a Gidan Dabo. Wannan abu ne da ya kamata ya yi duba ganin cewa yana cikin masu fafutikar ganin an ba mata hakkinsu yadda ya dace. Kazalika, ina rokon duk wanda zai taimaka mana a ko'ina cikin duniya ya taimaka kada mu mutu. Allah Ya tabi zuciyar mutane su taimake mu.

Tambaya: Mun zo karshen wannan tattaunawa, ko kina da wani abu da kike son karawa?

Kawai dai ina son in ce, ni kaina ba dadi nake ji ba, wadannan maganganun da nake yi, kuma ba ina yi ba ne don cin mutunci wani. Idan da ina da gida, ina da abin da zan iya biyan dukkanin bukatuna, ba zan yi haka ba. Wannan ai tozarci ne, babu wanda zai so a ce shi ne ke yin wannan abin. Amma dai bana son wahalar rayuwa ta kai ni kasa, babu wanda ya sani, gaskiya ba na jin dadin yin wadannan abubuwan ni kaina. Kuma fa su sani ba zan taba zama Sarki ba, saboda ni mace ce. Amma ina fatar mutane su ji kokena.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp