![]() |
Shugaban Hukumar zabe a Nijeriya INEC |
Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar kan harkokin zabe.
An amince da INEC da Naira biliyan 40 a cikin kasafin kudin 2024.Bukatar Naira biliyan 126 da shugaban hukumar ya yi, ya nuna karuwar sama da kashi kaso mai tsoka daga naira biliyan 40 da aka bai wa hukumar a 2024.
Mahmood ya ce hukumar na bukatar sama da Naira biliyan 126 a kasafin kudin shekarar 2025, kuma suna da takardu da za su bayar da cikakken bayani kan yadda za a kashe Naira biliyan 126 din.
Ya kuma bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar da su duba karin kudaden da hukumar ta bukata domin gudanar da ayyukanta.