Hukumar tace finafinai ta haramta wa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin fim ko waka a jihar Kano

Usman Soja Boy

 

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da Usman Sojaboy mawaki a Kannywood da wasu jarumai biyu Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan daga shiga duk wasu harkoki na Kannywood a Kano.


An yanke wannan hukuncin ne bayan wani faifan bidiyo da ya bayyana da ke nuna wasu dabi'u da ya sabawa addini, al’ada da dabi’un musulmi. A cewar hukumar ta samu korafe-korafe da dama daga al’umma da kuma malaman jihar.


A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa an sha gargadin Sojaboy akan abubuwa irin wa'yanda suka saba da tarbiyya da al'ada.


Sanarwar ta ce babban sakatare a hukumar tace fina-finan ta Kano,Abba El-Mustapha ya umurci sashin tantancewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman biyu ba su shiga cikin wani shiri da ake a Kannywood ba,ya ce hukumar ba za ta lamunci duk wani abu da ya sabawa tarbiyya ko al'ada ba don haka ta dakatar da su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp