![]() |
JAMB |
Babban jami'in hukumar da ke kula da harkokin hulda da jama’a, Dr Fabian Benjamin, ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce sauyin lokacin ya zama dole domin bai wa hukumar damar aiwatar da wasu muhimman gyare gyare ga tsarin yin rajistar.
Dr Fabian Benjamin ya kara da cewa hukumar JAMB ta gano cewa akwai wasu cibiyoyi na jarrabawa CBT da ake zargin suna amfani da kayan aikin da basu dace ba da yaudara, lamarin da ya jaddada bukatar yin bincike don kawo gyara ta hanyar kin amincewa da irin wadannan cibiyoyin.