Hukumar shirya Gasar Firimiyar kwallon kafa ta Najeriya ta bada hutun wasanni


Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya NPFL, ta ayyana hutun tsakiyar gasar bana ta 2024/25, na wasannin zagayen farko.

A cikin sanarwar da hukumar ta rabawa manema labarai, hukumar ta ce za a dawo hutun ne domin ci gaba da zagaye na biyu na gasar a ranar 25 ga Janairun 2025, bayan shafe makonni uku ana hutu.

Haka zalika hukumar ta bayar da damar bude cinikayyar 'yan wasa wato 'Transfer' daga Ranar 6 ga Janairu zuwa Fabrairu 5 ga watan 2005. 

Kungiyar Remo Stars ce ke jagorancin teburin gasar da maki 36, yayin da Rivers United ke rufa mata baya da maki 34.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp