Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Legas, ta ce ta kama wasu mutane 38 da ake zargi da safarar kwayoyi tare da kwace kilogiram 339,576.91 na kwayoyi a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar Mitchell Ofoyeju , ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Legas.
Magungunan da aka kama sun hada da Codeine , Tapentadol , Tafradol , da Benzhexol
Sauran sun hada da Cannabis Indica da Methamphetamine sai Cocaine sauran su.