Hukumar yaki da safarar mutane a Nijeriya NAPTIP ta ce jami'anta sun ceto wasu mata masu ciki 9 da ke tsare a wani gida cikin birnin tarayya Abuja.
Wata sanarwa da jami'in yada labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye ya fitar, ya ce gidan yin jariran yana unguwar Ushafa cikin Abuja.
A cewar Adekoye, kamen ya biyo bayan wani samame da jami'an NAPTIP suka kai bayan an kwarmata musu bayanin gidan.