Hukumar kwastam a Nijeriya ta kama fetur da ya kai lita 199,495 a jihar Adamawa

 

Hukumar Kwastam


Hukumar kwastam a Nijeriya da ke kula da shiyyar Adamawa da Taraba ta kama litar man fetur da ya kai 199,495 daga hannun masu fasa kwauri a kan iyakar kasar Kamaru.

Shugaban hukumar, Bashir Adeniyi ya jagoranci ‘yan jarida domin duba kayayyakin da suka kama, ya ce wannan ne karo na uku da aka kama tun bayan kafa rundunar ‘Operation Whirlwind’ a jihar a watan Mayun shekarar 2024.

Adeniyi ya kara da cewa jami’an hukumar kwastam sun kama adadin man fetur din da aka nuna a yayin gudanar da ayyukan su a shiyya da ke Adamawa da Taraba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp