Hukumar kula da 'yan sandan Nijeriya ta umurci duk wani jami'i da ya haura shekaru 60 da yayi ritaya

 

Kayode Egbetokun

Umurnin na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da jaridar Daily Trust ta yi rahoto kan wani sabon cece kuce da ya kunno kai a cikin rundunar 'yan sandan kan karin wa’adin aikin da aka yi wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun bayan ya cika shekaru 60. 

A cikin wani sabon rahoto da jaridar ta buga a ranar Juma’a, hedikwatar rundunar tare da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, sun tabbatar da cewa ci gaba da zaman Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na 'yan sandan yana kan doka.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, kakakin hukumar ta hukumar kula da 'yan sandan Nijeriya PSC, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa wannan matakin ya zama tilas saboda hukumar ba ta son ya zama ana saba wa doka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp