Hukumar lura da shige da fice ta Najeriya Immigration a jihar Jigawa ta kubutar da mutum 10 da ake zargin an yi safarar su ya yin wani samame da ta kai a karamar hukumar Babura.
Shugaban hukumar a jihar CIS Musa ne , ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema Labarai a ofishin sa dake birnin Dutse.
Ya ce bayan samamen da aka kai mai taken 'Operation Salama' a Naira Tsamiyar Kwance a Babura, an kubutar da Mata 8 sai Maza biyu da ke kan hanyar zuwa Turai.
CIS Musa, ya ce wadan da aka yi safarar su matasa ne da shekarun su ke tsakanin 21 zuwa 30, kuma sun fito ne daga jihohin Ogun sai Oyo da Ondo da kuma Imo.