Hukumar kula da harkokin shari’a a Jigawa ta sallami ma’aikatanta uku bisa rashin ɗa’a

 


Hukumar da ke kula da harkokin shari’a a jihar Jigawa ta kuma umurci wasu alkalan kotunan shari’ar Musulunci guda uku da su yi murabus, tare da dakatar da wasu biyu.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar Abbas Wangara ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce hukuncin ya biyo bayan taron hukumar karo na 178 wanda ya amince da matakin ladabtar da ma’aikatan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp