Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda a Nijeriya PSC ta sallami jami’an ‘yan sanda guda biyu, ta kuma rage wa wasu guda shida matsayi bisa wasu zarge zarge

Police


Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta amince da korar wasu mataimakan Sufiritanda 'yan sanda guda biyu bisa zargin su da laifukan rashin da’a, almundahana da zagon kasa.Hukumar ta kuma amince da rage wa wasu jami’ai shida mukamai bisa laifuka irin nasu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda Ikechukwu Ani, ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce hukumar ta kuma amince da hukunci mai tsanani ga wasu manyan jami’an ‘yan sanda guda goma da aka samu da laifin cin amana da zagon kasa.

A cewar sanarwar hukumar ta amince da hakanne bisa bincike da ta gudanar kan korafe korafen da akai ga jami'an.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp