![]() |
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa |
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da kamen ga jaridar PUNCH a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa jami’an Hisbah sun kai farmaki gidan abincin ne a daren ranar Larabar, biyo bayan samun bayanan sirri.
Ya ce abin takaicin ma shine saurayin tare da abokan sa ne suka gudanar da daurin auren a gidan abincin ba tare da amincewar iyayen su ba.
Ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta zuba ido tana kallon ana yin wasu abubuwan da basu dace ba, da za su keta shari’a a fadin jihar.