![]() |
Jami'an hukumar NDLEA |
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kano ta ce ta kama mutane 1,345 da ake zargi da kuma kama wasu haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram dubu 8.430.239 a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a Kano.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 1,301 da mata 44, ya kara da cewa haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da hodar iblis, magungunan tari, da allurar tramadol na sama miliyan biyar.
A cewarsa, a kokarin da suke na hana shan kwayoyi a jihar Kano, sun kaddamar da ‘Operation Hana Maye’ da nufin yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma samar da yanayi mai kyau ga al'ummar jihar.